WASWASI (KOKONTO) [DEPRESSION] DA KUMA HANYOYIN WARWARE SHI
YADDA AKE MAGANCE SU A MUSULUNCE!!! Zan fara da faɗin Allah Ta'ala: قل أعوذ برب الناس. ملك الناس. إله الناس. من شرالوسواس الخناس. ألذى يوسوس فى صدورالناس. من الجنة والناس. Fassara: "KACE! INA NEMAN TSARI DAGA UBANGIJIN MUTANE. MAMALLAKIN MUTANE. UBANGIJIN MUTANE. DAGA SHARRIN MAI SANYA WASWASI MAI ƁOYEWA. (SHINE) WANDA YA KE SANYA WASWASI A CIKIN ƘIRJIN MUTANE. DAGA ALJANNU DA MUTANE. Haka kuma Allah maɗaukakin sarki yana faɗa a cikin Suratul Baƙarah: ولنبلونكم بشيء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والأنفس والثمرات وبشرالصابرين. ألذين إذا أصابتهم مصيبة قالوا إنا لله وإنا إليه راجعون. Fassara: "WALLAHI ZAMU JARABCE KU DA WANI ABU DAGA TSORO DA YUNWA DA RASHIN DUKIYOYI DA NA RAYUKA DA ƳAƳAN ITACE, KA YI WA MASU HAƘURI BUSHARA. SUNE WAƊANDA IDAN MUSIBA TA SAMESU ZA SU FAƊA 'LALLAI MU GA ALLAH MUKE KUMA GARESHI ZAMU KOMA'. *ƘARIN BAYANI:* |. Wannan Surah da muka ambata, Allah na yi mana nuni da mu riƙa neman tsarin Allah a kan Sharrin Mutum da na Aljan, kuma lallai WA...