WASWASI (KOKONTO) [DEPRESSION] DA KUMA HANYOYIN WARWARE SHI





YADDA AKE MAGANCE SU A MUSULUNCE!!!

Zan fara da faɗin Allah Ta'ala:
قل أعوذ برب الناس. ملك الناس. إله الناس. من شرالوسواس  الخناس. ألذى يوسوس فى صدورالناس. من الجنة والناس.
Fassara:

"KACE! INA NEMAN TSARI DAGA UBANGIJIN MUTANE. MAMALLAKIN MUTANE. UBANGIJIN MUTANE. DAGA SHARRIN MAI SANYA WASWASI MAI ƁOYEWA. (SHINE) WANDA YA KE SANYA WASWASI A CIKIN ƘIRJIN MUTANE. DAGA ALJANNU DA MUTANE.

Haka kuma Allah maɗaukakin sarki yana faɗa a cikin Suratul Baƙarah:
ولنبلونكم بشيء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والأنفس والثمرات وبشرالصابرين. ألذين إذا أصابتهم مصيبة قالوا إنا لله وإنا إليه راجعون.
Fassara:
"WALLAHI ZAMU JARABCE KU DA WANI ABU DAGA TSORO DA YUNWA DA RASHIN DUKIYOYI DA NA RAYUKA DA ƳAƳAN ITACE, KA YI WA MASU HAƘURI BUSHARA. SUNE WAƊANDA IDAN MUSIBA TA SAMESU ZA SU FAƊA 'LALLAI MU GA ALLAH MUKE KUMA GARESHI ZAMU KOMA'.


*ƘARIN BAYANI:*

|. Wannan Surah da muka ambata, Allah na yi mana nuni da mu riƙa neman tsarin Allah a kan Sharrin Mutum da na Aljan, kuma lallai WASWASI daga sheɗanu ne.

||. Ayar da muka ambata a sama kuma mun kawo ta ne domin mu sani cewar dukkan wata matsala ta Waswasi ko na ce cutar Depression (wato shiga Damuwa) tana da alaƙa ne da Jarabtar da Ubangiji ya yi alkawarin zai yi wa bayinsa. Kuma zamu ga dukkan Wata matsala da ta jefa mutum cikin waswasi ko ciwon samuwa daga cikin wadannan jarabawowin ne guda 5 da Allah ya faɗa ya kuma yi alkawarin sai ya riƙa jarabtamu a kansu, kuma babu wani a duniyar nan da zai ce ya tsallake waɗannan musibobi a rayuwarsa ko wanene. Don haka, duk wanda ya samu kanshi cikin wata musiba ya yi haƙuri ya kuma yawaita ISTIRJA'I, domin kuwa Allah yana sane da shi, kuma zai ya ye masa musibar ya kuma ba shi lada idan ya yi haƙuri.

*Minene WASWASI?*
shine mutum ya ji a ransa ya yi wani abu ko kuma bai aikata wani abu ba, wanda a sanadiyar hakan zai riƙa shiga cikin damuwa, da ƙunci da kuma rashin samun nutsuwa a rayuwarsa.

Waswasi ciwone marar daɗi kuma  idan ya yi yawa yakan yi sanadiyar raba mutum da imaninsa ko ɗora mutum zuwa ga hanyar da zai rasa rayuwarsa.
Waswasi dai sheɗan ne ke haddasa shi, kuma babban maganinsa shi ne yawaita Isti'aza.

Waswasi (kokonto) ya kasu gida uku:-

1. WASWASI ACIKIN IBADAH DA DABI'ANTUWAR RAYUWA: Akwai wanda shi dama waswasin ya zamo masa ciwo babu abinda zai yi face akwai waswasi a cikin sa. Irin wannan nau'in sai an dage sosai kana a samu maganinsa, domin shine ke kai mutum ga rasa imani ko ya rasa rayuwarsa ta hanyar   halakar da kansa. Irin wannan waswasin har Kore samuwar Allah yake yi, wanda idan da mutum zai furta abin da yake waswasin a cikin zuciyarsa; toh da za a iya yi masa haddi na riddah.

2. Akwai kuma Wanda waswasin da ya ke yi, ya samu ne sanadiyar saɓon Allah da ya ke yi, kuma maganin hakan shine tuba ga Allah, tare da dai na saɓawa Allah ɗin.
3. A kwai kuma wanda waswasin sa ya ginu ne, avkan rashin sani na wasu ilmummuka da suka shafi addini.

*HANYOYIN SAMU WARAKA DAGA CUTAR WASWASI SUNE KAMAR HAKA:-*

1- Neman tsarin Allah da kuma jin tsoronsa (wato Taƙawa)
Duk Wanda ya samu kansa cikin halin yawan waswasi da damuwa (depression) babban hanyar sa ta farko shine KIYAYE ABINDA ALLAH DA MANZONSA SU KA YI UMURNI DA SHI GWARGWADON IKONSA DA KUMA BARIN ABINDA ALLAH DA MANZONSA SUKA HANE SHI (domin duk abinda aka hani mutum to zai iya hanuwa a kansa, amma Wanda aka umurci mutum da ya aikata, Sai dai mutum ya yi bakin ƙoƙarinsa gwargwadon imaninsa ga Allah, wurin aiwatarwa sai kuma ya cigaba da neman gafarar Allah S.W.T.).

Mai fama da wannan matsalolin ya sani, Allah ya yi alkawarin duk wanda ya ji tsoron sa, toh zai sanya masa mafita, kuma zai taimake shi a kan kowanne irin Sharri na shaiɗan.

2. Yawan Ambaton Allah: wajibine mai son ya samu sauƙi daga matsalar waswasi/kokonto/depression ya yawai ta ambaton Allah, musamman Salati ga Manzon Allah S.A.W, Istigfari, fadar INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN, sannan duk sadda waswasi ya bijiro masa akan abinda ya shafi imaninsa ga Allah ko ga Manzonsa S.A.W ya rinƙa karanta "ALLAHU AHAD, ASSAMADU ALLAZEE LAM YALID WALAM YULAD WALAM YAKUN LAHU KUFUWAN AHAD, HUWAL AUWALU WAL AKHIRU WAZ ZAHIRU WAL BAƊINU WAHUWA BI KULLI SHAI'IN ALEEM"

3- Haka kuma mai fama da ciwon waswasi ya kasance ya dogara ga Allah da yawan karatun Alƙur'ani da kuma sauraronsa, ya rinƙa karanta tarihin musulunci ko sauraren tarihin Annabawa da bayin Allah salihai.

4. Ana buƙatar mai ciwon waswasi ya daina yawan zama shi kaydai, da yawan tunanin abin duniya.

5. Ya yawaita Addu'a da abota da mutanan kirki da kuma rashin yarda da duk abinda zuciya ta ayyana masa.

6. *MAGANI:*
Bayan mai ciwon yabi waɗannan hanyoyi na sama waɗanda sune za su taimaka masa kan maganin da zai yi ya yi tasiri, amma matuƙar ba a kiyaye su ba, toh maganin da za a yi ba zai yi tasiri ba.

Ga magungunan da za a nema:

1. A nemi garin Safarjal da garin Ƙirifat (girfa), garin Habbatussauda, Garin Zaitun Sai kuma Zuma.

Za a ɗebi cokali ɗaya ƙarami na garin Ƙirifat (girfa) Sai na garin Safarjal shima cokali 1, Sai garin habbatussauda da na Zaitun kowannensu cokali ɗaya, Za a motse su kana a zuba Zuma Sai a raba su kashi uku, a sha kashi ɗayan da safe Sai sauran kashin  kuma a sha da rana da kuma dare. 
 Asha maganin Tsawon sati 2.

2. A nemi turaren Hububul Miski ko kuma farin miski da turaren Ambar (mi'a sa'ila), sai Man Simsim da Man Zaitun ya haɗe su guri ɗaya cikin wata babbar kwalba, ya kuma tofa:
 S. Fatiha × 7.
S. Kafirun × 3.
S. Ikhlas × 3.
S. Falaƙ × 3.
 S. Nass × 3.

Sai kuma a karanta wannan addu'o'i:

 1. A'UZU BILLAH WAƘUDRATIHI MIN SHARRI MA'AJIDU WA UHAZIRU (×3).
2. A'UZU BIKALIMATILLAHI TAAMMAATI MIN SHARRI MAKHALAQ (×3).
3.BISMILLAHILLAZE LAYA DURRU MA'ASMIHI SHAY-UN FIL ARDI WALA FISSAMA'I WAHUWAL SAMI'UL ALEEM (×3).
4. LA ILAHA ILLALLAHUL AZEEMUL HALIMU, LA ILAHA ILLALLAHU RABBUL ARSHIL AZEEM, LA ILAHA ILLALLAHU RABBUS SAMAWATI WA RABBUL ARDI WA RABBUL ARSHIL KAREEM.
5.RABBUNALLAHUL LAZEE FIS SAMA'I TAƘADDASA ISMUKA, AMRUKA FISSAMA'I WAL ARDI, KAMA RAHMATUKA FIS SAMA'I FAJ-AL RAHMATAKA FIL-ARDI, IGFIRLANA HUBANA WAKHATAYANA ANTA RABBUT TAYYIBEEN, ANZIL RAHMATAN MIN RAHMATIKA, WASHIFA'AN MINbSHIFA'IKA ALA HAZAL WAJ-E FAYAB-RA'U (×3).
6. ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WA'ALA ALI MUHAMMADIN KAMA SALLAITA ALA IBRAHIMA WA ALA ALI IBRAHIMA FIL'ALAMINA INNAKA HAMIDUN MAJEED.

Sai ya tofa a ciki, zai riƙa shafawa ga jikin sa, musamman da safe da kuma dare.
Allah ya yi mana tsari daga Sharrin mutum da Aljan amin.

Fuad Islamic Herbal Medicine Misau

No. 2. Tamsuguri Turaki Street Misau Bauchi State Nigeria.

+2349031562132
+2348067676223
+2348024508141

Comments

Popular posts from this blog

AMFANIN SHAMMAR GA MATA TA ƁANGAREN NONO

BRAIN BOOSTER