FA'IDODIN TURMERIC (KURKUM) GA ƊAN ADAM
*_Shin a na yin amfani da Turmeric (kurkum) ta fuskar magani da ƙara lafiya ajiki?_* Haƙiƙa ana amfani da shi, amma ba za mu ƙara fahimtar haka ba sai mun ɗan karanta ɗan ƙaramin bayani a kansa da wasu fa'idodinsa. Kar kumanta yana da kyau mu koya ma kanmu da matan mu da ƴaƴan mu amfani da wasu itatuwa a abinci, musamman a lokacin da za a dafa abinci waɗannan itatauwa sune kamar haka: Ɗanyar Vitta, Ɗanyar kurkur, ɗanyar tafarnuwa. Musamman ɗanyar citta da ɗanyar tafarnuwa domin suna taimaka wa wajen ƙara lafiya da kuma kariya da kamuwa da wasu cutuka dake kama hanji. TURMERIC yana ɗauke da wasu sinadarai masu yawa a cikin sa yana ɗauke da sinadarin *anti-inflamantrey* da *antioxidant*. Kuma a cikin sa ya haɗa da sinadarin curcumin, don haka a na iya amfani da turmeric don kula da lafiyar al'aura. Don haka yana kawar da wasu cututtuka kamar: Kumburin gaba, da ƙurajen gaba da sauransu. Yana da kyau u san waɗannan fa'idodin da turmeric take yi ga lafiyar farji: ...