FA'IDODIN TURMERIC (KURKUM) GA ƊAN ADAM
*_Shin a na yin amfani da Turmeric (kurkum) ta fuskar magani da ƙara lafiya ajiki?_*
Haƙiƙa ana amfani da shi, amma ba za mu ƙara fahimtar haka ba sai mun ɗan karanta ɗan ƙaramin bayani a kansa da wasu fa'idodinsa.
Kar kumanta yana da kyau mu koya ma kanmu da matan mu da ƴaƴan mu amfani da wasu itatuwa a abinci, musamman a lokacin da za a dafa abinci waɗannan itatauwa sune kamar haka: Ɗanyar Vitta, Ɗanyar kurkur, ɗanyar tafarnuwa. Musamman ɗanyar citta da ɗanyar tafarnuwa domin suna taimaka wa wajen ƙara lafiya da kuma kariya da kamuwa da wasu cutuka dake kama hanji.
TURMERIC yana ɗauke da wasu sinadarai masu yawa a cikin sa yana ɗauke da sinadarin *anti-inflamantrey* da *antioxidant*.
Kuma a cikin sa ya haɗa da sinadarin curcumin, don haka a na iya amfani da turmeric don kula da lafiyar al'aura. Don haka yana kawar da wasu cututtuka kamar: Kumburin gaba, da ƙurajen gaba da sauransu.
Yana da kyau u san waɗannan fa'idodin da turmeric take yi ga lafiyar farji:
Fitattun fa'idodin turmeric ga al'aura sune kamar haka:
1. *Maganin Fungus na Farji*.
Curcumin na iya taimakawa wajen kashe yeast na Candida, ko kuma zai iya rage haifuwarsu, saboda yana hana su mannewa ga sel, don haka yana iya ba da gudummawa ga maganin ciwon farji, wato yeast infection, to wannan sinadarin na curcumin a kwai shi a cikin Turmeric (Kurkur)
Yin shayinsa yana taimakawa wajen yaƙar wasu manyan cututtuka kamar: Colon cancer, Prostates cancer, ko Colon of the disease.
Yana taimakawa wajen kewayawar jini, yana ƙara ma garkuwar jiki ƙarfi.
Yana sauƙaƙa matsalolin ciwon ƙashi daban-daban daban.
Yana yaƙar taruwar yawan kitse don haka yake saukaika yawan ƙiba da nauyi.
Kurkur yana ɗauke da sinadarin anti-bacteria, sannan yana hana yawan bushewar jiki musamman ga mata.
Yana sauƙaƙa matsalar data shafi gaba ɗaya hanyoyin mafitsara wato Urinary system tun daga cikin ƙoda har zuwa al'aura baki ɗaya.
Hakanan a na iya amfani da Turmeric don magance cututtukan da ke shafar farji, wanda ke haifar da zafi da ƙaiƙayi, saboda yana iya rage jin ƙaiƙayi a cikin farji.
2. *Sauke alamun PMS*
Yin amfani da ruwan ƴaƴan itace na turmeric zai iya taimakawa wajen rage zafi, da wasu matsalolin saboda sinadarin anti-inflamantry dake ciki.
Amfanin turmeric ga farji dangane da yanayin haila shima yana iya kasancewa yana taimakawa:
Rage wasu alamomin da ke haifar da canjin yanayi, kamar:
Kumburi, Damuwa, Ciwon kai, Rashin kuzari, daidaita matakan hawan haila.
Domin samun fa'idar da ake samu ta hanyar rage raɗaɗin jinin al'ada, za a iya shan ƙaramin cokali guda ɗaya tare da madara ko zuma, sannan a ci gaba da wannan al'amarin a kullum har tsawon kwanaki 7 kafin jinin al'ada da kuma kwana 3 bayan gama al'adar.
Amma akan iya haɗa shi da wasu magungunan kamar Ginger domin ƙara ƙarfi.
*Gargadi*:
A kula da wannan banda shansa adadi mai yawa musamman idan shi kaɗai ne musamman ga mata masu ciki juna biyu, da kuma masu shayarwa, sai dai wanda aka haɗa da wasuvitatauwa,vshima kaɗan kaɗan ake shansa, sakamakon akwai bambancin da wanda za a sha zalla.
*Gargadi na biyu*
Kada ayi amfani da wanda aka mayar dashi powder, ko aka yi masa tiriri tare da wasu abubuwan, ɗanye za a samo sannan a wanke a kankare kuma, idan ana buƙatar garin sa sai avyanka shi sannan a busar da shi.
Amma mu kula amfani da ɗanyan sa yafi bada fa'ida sosai, sannan musamman a haɗa shi da wasu itatuwa daban to faidan sa yana ninkawa sosai.
Fatan alkhairi gare ku baki ɗaya.
Domin karin bayani wannan shine WhatsApp number ɗin mu.
09031562132
Fuad Islamic Herbal Medicine Misau.
No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau, Bauchi state Nigeria.
09031562132
Comments