AMFANIN SHAMMAR GA MATA TA ƁANGAREN NONO

AMFANIN SHAMMAR GA MATA


Fuad Islamic Herbal Medicine Misau.

Haƙiƙa gaskiya ne nono ado ne a wajen mata, domin rashinsa ko ƙanƙancinsa tawayane a wajensu, kuma maganan gaskiya sunfi jan hankalin mazajensu idan mace tana da shi dai dai gorgodon hali.

Saboda haka nakeso ƴan uwa mata ku mayar da hankali ku fahimci wannan bayani sosai.

Gyaran nono a wajen mace ya kasu kashi uku:

Na farko:

- Rashinsa ko kyankancinsa tana so ya ƙara girma.

Na biyu kuma:

- Girmansa ya yi yawa sosai tana so ta rage shi ya koma madaidaici saboda girman yasa nonon har ya zube kamar mai shekaru Arba'in gata kuma shekarunta kaɗan, ko kuma budurwace ma bata taɓayin aure ba gashi har nononta ya zube.

Na uku kuma:

- Ya kwanta gaba daya tana so ya miƙo ya koma kamar ta ƴar budurwa ƴar  sha bakwai.

To lalle ku sani kowanne daga cikinsu waɗannan kashin da muka kawo akwai abubuwa da za a yi amfani da su kuma a samu biyan buƙata cikin sauƙi, don na kula yawancin mata suna da ƙishir ruwan irin wannan bayanin amma kunya yana hana su tambaya.

Bari mu yi bayani akan na farkon ataƙaice sannan daga bisani abimu bashin sauran.

Abu na farko shine matsalan ƙanƙancewar nono wanda shi akafi buƙata ma akan sauran biyun, don haka ga hanya mai sauƙi da zaki samu cikakkiyar mama ba tare da kinsha wahala ko kin kashe kuɗi ba.
Ki samu garin SHAMMAR (fennel ) da ɗan dama wanda zai kai ki kamar wata kina amfani da shi sai kike ɗiban tea spoon ɗaya kina zubawa a cikin ruwan dumi kofi ɗaya kina sha safe da yamma.
Sannan ki samu man HULBA da MAN GELO (CASTOR OIL) ki haɗa a waje ɗaya sai ki garwaya, idan ki ka haɗa su a waje ɗaya sai ki na shafawa a nonon gaba ɗaya sau biyu a yini.

Sa'annan ki samu rigan mama dai-dai ƙirjinki kada ya matse kuma kada ya yi yawa.

Insha Allahu cikin lokaci ɗan ƙanƙani za ki ga nononki ya cicciko yadda ki ke buƙata, amma za ki daina amfani da maganin idan ki ka samu biyan buƙata kar kuma girman ya yi yawa sosai yadda zayyi saurin zubewa.

NB:  Duk abin da na faɗa na magunguna ana samun shi a wajen masu sayar da Islamic Medicine.
Sa'annan ga hoton Shammar ɗin  saboda kar a baki wani abu daban, kuma idan aka baki ki shinshina ki ji saboda Shammar na asali yana da ƙamshi kamar turare, idan aka baki wanda baya ƙamshi to bashi bane.

Fatan mu shine har kullum Allah ya mana dace gaba ɗaya ya kuma ƙara mana lafiya ya bawa marasa lafiya lafiya.


Fuad Islamic Herbal Medicine Misau

No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau kusa da gidan Marigayi Alhaji Ahmed Katibu Misau.

09031562132
08967676223
08024508141

Comments

Popular posts from this blog

WASWASI (KOKONTO) [DEPRESSION] DA KUMA HANYOYIN WARWARE SHI

BRAIN BOOSTER