AMFANIN MAN ZAITUN GA ƊAN ADAM
Da sunan Allah mai yawan Rahmah mai yawan jin ƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaba, farin jakada, Annabi Muhammad Sallallāhu alayhi wa Sallam da Ahalin gidan sa zaɓaɓɓu da sahabban sa masu girma baki ɗaya. *ZAITUN DA MAN ZAITUN* Haƙiƙa zaitun itaciya ce mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin ɗan Adam, kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayanin ta a cikin Littafin Allah mai Tsarki (Alƙur'ani), haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam. An samu daga sayyadina Umar Allah ya ƙara masa yarda yana ce wa: Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam ya ce: *"Kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafa shi a jikin ku, domin haƙiƙa shi yana daga cikin bishiya mai albarka.* Tirmizhy ne ya ruwaito shi. *KAƊAN DAGA CIKIN AIKIN DA ZAITUN YAKE YI GA LAFIYA SUN HAƊA DA:* ́ 1. *ƘARFIN MAZAKUTA* Duk mutumin da ya samu kan shi a wannan hali, to ya samu garin habbatus...