AMFANIN MAN ZAITUN GA ƊAN ADAM
Da sunan Allah mai yawan Rahmah mai yawan jin ƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaba, farin jakada, Annabi Muhammad Sallallāhu alayhi wa Sallam da Ahalin gidan sa zaɓaɓɓu da sahabban sa masu girma baki ɗaya.
*ZAITUN DA MAN ZAITUN*
Haƙiƙa zaitun itaciya ce mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin ɗan Adam, kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayanin ta a cikin
Littafin Allah mai Tsarki (Alƙur'ani), haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam.
An samu daga sayyadina Umar Allah ya ƙara masa yarda yana ce wa:
Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam ya ce:
*"Kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafa shi a jikin ku, domin haƙiƙa shi yana daga cikin bishiya mai albarka.*
Tirmizhy ne ya ruwaito shi.
*KAƊAN DAGA CIKIN AIKIN DA ZAITUN YAKE YI GA LAFIYA SUN HAƊA DA:*
́
1. *ƘARFIN MAZAKUTA*
Duk mutumin da ya samu kan shi a wannan hali, to ya samu garin habbatus sauda ya dinga zubawa a cikin ruwan ɗanyan ƙwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci Kullum, in shaaAllah zai samu ƙarfin mazaƙuta sosai.
Kada a gaji duk wani magani da aka gani a gwada za a dace in shaaAllah.
2. *CIWON CIKI*:
Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya haɗa da garin habbatus sauda ya cakuɗa ya sha safe da yamma.
A samu kamar sati ɗaya ana sha in shaaAllah.
3. *CIWON KAI*
Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kan sa yana kuma shan cokali ɗaya da safe da rana da dare in shaaAllah za a samu lafiya.
4. *CIWON HAƘORI*
Duk mutumin da yake ciwon haƙori sai ya samo ganyen Zaitun da ƴaƴan habbatus sauda a saka su a cikin garwashi sai a bude baki hayaƙin ya dinga shiga, in shaaAllah za a samu lafiya.
5. *CIWON HANTA*
Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali ɗaya da safe ɗaya da Rana ɗaya da dare.
6. *CIWON DASASHI*
Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakin sa da shi.
7. *TARIN FUKA*
Duk Wanda yake tarin fuka to sai ya dinga shan man zaitun ya haɗa da man Tafarnuwa, man habba, man Ma'ana, man Albasa, ma'u Khal, da Zuma, sai ya haɗa su waje ɗaya ya rinƙa shan cokali ɗaya da safe, ɗaya da rana, ɗaya da daddare.
In shaaAllahu za a samu lafiya.
8. *CIWON SUKARI (DIABETES)*
Duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana haɗawa yana sha kafin ya kwanta bacci in shaaAllah zai warke.
9. *CIWON ASMA (ATHMA)*
Duk mutumin da wannan ciwon ya kama shi ,to sai ya samu ganyen zaitun ko "ƴaƴan sa ya dinga turara wa.
10. *CIWON ƘODA*
Duk mutumin da yake ciwon ƙoda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana in shaaAllah.
11. *CIWON BAYA*
Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatus sauda a kwaɓa ya dinga shafawa a bayan in shaaAllah zai warke.
12. *CIWON RAMA*
Duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku in shaaAllah zai yi ƙiba.
*Ƙarin bayani:*
Amma a rage yawan tunani da ɓacin rai.
13. *ZAZZAƁI MAI ZAFI*
Duk mutumin daya kamu da zazzaybi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali ɗaya sannan yana karanta Āyatul Kursiyyu sau 7 yana tofawa a cikin ta yana shafe jikin sa da ita in shaaAllah.
14. *KYAWUN FUSKA*
Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, tayi fari Wanda ba zai cutar da shi ba, to ya dinga shafa man zaitun da na habbatus sauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe sai ya wanke da sabulun salo zai yi mamakin yadda fuskar sa za ta koma.
15. *ZUBEWAR GASHI*
Duk macen da gashin ta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube, to sai ta samu ruwan zafi ta wanke kan ta da shi sannan bayan ya ɗan bushe sai ta zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kan na ta da shi gaba ɗaya kullum.
16. *ƘARANCIN JINI*
Duk mutumin da yake da ƙarancin jini a jikin sa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a Rana.
17. *BAYAN GIDA MAI ƘARFI (WATO BASUR)*
Duk mutumin da yake shan wahala in yazo zai yi bayan gida, wani ma sai Yayi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatus sauda ya kwabia sai ya turashi a cikin duburar sa in shaaAllah bayan gidan sa zai rinƙa fita da laushi ba wahala.
18. *CIWON MARA GA MATA*
Duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara saboda fitar jini in tana so ta samu sauƙin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana haɗawa da hulba, da ƙusdul Hindi da ruwan tsamiya tana sha, in shaaAllah duk lokacin da za tayi haila ba zai Mata ciwo ba.
19. *SANYIN ƘASHI*
Duk mutumin da ƙashin sa yayi sanyi baya iya motsa shi, to sai ya samu man zaitun da man habbatus sauda ya dinga sha yana kuma shafawa a wajan in shaaAllah.
20. *KYAWUN FATA DA LAUSHINTA*
Duk mutumin da yake so fatar sa tayi laushi da kyau, to sai ya sami man zaitun ya dinga shafe jikin sa da shi bayan Yayi wanka da ruwan ɗumi, zai yi mamaki yadda fatar sa za ta koma da izinin Allah.
21. *ƘURAJEN ƘARZUWA (QAZUWA)*
Duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu ƙuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyan zaitun ya ƙirba shi ya hada da garin habbatus sauda yana shafawa a wajan har ya warke.
22. *CIWON KUNNE*
Duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya Bari in zai kwanta bacci sai a dinga hadya man zaitun da na habbatus sauda yana ɗigawa a kunnen sa a toshe da auduga in shaaAllah zai samu lafiya.
23. *CUTAR KYASFI*
Duk mutumin da yake da KYASFI a jikin sa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe, ya daka shi yayi laushi sai ya haɗa shi da man zaitun ya cakuɗa, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci, sai ya wanke in ya farka daga barci.
24. *SHAFAR ALJANU*
Duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu basa son shi, shi da habbatus sauda.
Ku dubu rubutuna kan Matsalolin Aljanu da yadda za a magance su ta nan wajen 👇
http://fuadislamicherbalmedicinemisau1.blogspot.com/2021/11/matsalolin-aljanu-da-yadda-za-magance-su.html
Dan haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da su a ko wane lokaci, in da hali ma ya mai da su man sa na shafawa da kuma zubawa a abinci ko abin sha, amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta Āyoyin ruƙyah da kuma Azhkārai waɗanda suka tabbata a Sunnah.
25. *CIWON KARKARE (DAN KANKARE)*
Duk mutumin da ciwon karkare ya same shi, to sai ya samu man zaitun, sannan a samu lalle a kwaɓa, sai a zuba man zaitun din a cikin lallen a gauraya, sannan a karanta (ĀYATUL KURSIYYU) sau 7 a tofa a ciki sannan sai a tofa a jikin wannan karkare in shaaAllah.
26. *CIWAN NONO*
Duk matar da take fama da ciwan nono saboda rashin zubar sa, to ana haɗa man zaitun da garin sa, a barbaɗa a kan nonon saboda samun damar zuba, dan ƙofofin su bude.
27. *MOTSA SHA'AWA*
Man zaitun yana motsa sha'awa in an shafa shi a lokacin da za ayi mu'amalar aure ga masu aure in shaaAllah.
28. *CIWON SAIFA*
Duk mutumin da yake ciwon saifa, sai ya haɗa man zaitun da garin habbatus sauda da kuma Zuma farar saƙa ya riƙa sha, in shaaAllah.
29. *TSUTSAR CIKI*
Duk mutumin da yake fama da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatus sauda da zuma ya kwaɓa su ya riƙa sha, wannan tsutsar zata mutu da yardar Allah.
30. *CUTAR HANJI (ULCER)*
Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatus sauda kamar cokali ɗaya sannan ya samu garin (khumasari)da ganyan zaitun mai laushi ya jiƙa su ya dinga sha har sai ya warke.
31. *FITSARIN KWANCE*
Duk yaron da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun da kuma garin habbatus sauda a zuba a nono a riƙa bashi yana sha zai daina in shaaAllah.
32. *MUTUWAR JIKI (YAWAN KASALA)*
Duk mutumin da jikin sa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda da na zaitun zai ji kyarfin jikin sa in shaaAllah.
33. *YAWAN ZAZZAƁI*
Duk mutumin da yake yawan yin zazzaɓi, to sai ya samu garin habbatus sauda da na zaitun kamar cikin ludayi ya kwaɓa da ruwan zafi, da kuma zuma maras haɗi ya dinga sha in shaaAllah zai warke.
34. *CUWON GAƁOƁI*
Duk mutumin da gaɓoɓin sa suke masa ciwo to sai ya samu garin habbatus sauda da na Zaitun da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatus sauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a gabobin.
35. *ƘWARƘWATA*
duk matar da take fama da matsalar ƙwarƙwata, to ta samu man zaitun da garin habbatus sauda ta kwaɓa sannan sai ta bari sai Rana ta take sai ta zuba wannan man a kan ta ta bar shi yayi kamar minti (20) sannan sai ta wanke in shaaAllah za tayi ban kwana da ƙwarƙwata kuma za taga a abin mamaki.
36. *CIWON TARI*.
Duk mutumin da ya kamu da ko wane irin Tari to sai yayi kamar yadda na ambata akan batun TARIN FUKA, sai ya haɗa da citta da tsamiya, sai ya haɗa su guri ɗaya ya cakuda ya dinga amfani da shi in shaaAllahu zai warke.
37. *MAJINAR KIRJI*
Duk mutumin da yake fama da yawan majinar ƙirji to sai yayi kamar yadda na yi bayanin kan Tarin Fuka da Mura in shaaAllahu zai samu lafiya.
FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE MISAU
NO. 2. TAMSUGURI TURAKI STREET MISAU BAUCHI STATE NIGERIA.
+2348067676223
+2349031562132
Comments