MAGANIN RIKICEWAR JININ AL'ADA NA MATA
Rikicewar jinin Al'ada ga mata wannan ba baƙuwar matsala bace ko sabuwa ba.
Yawancin mata na fama da irin waɗannan matsalolin, sai dai sukan shiga cikin duhu, su kasa gane dalilan hakan.
Matsalar RIKICEWAR jinin Al'ada yana iya faruwa da kowacce mace me aure ce ko marar aure bazawara ko budurwa duka.
Sai dai kowacce akwai dalilin faruwar nata.
Yawanci Matsalar tafi damun Matan aure sakamakon yin allurar ko shan maganin tsarin ƙayyade iyali, saboda Waɗannan magungunan ko allurar ko wannan abin da ake cusa musu a wata jijiya a hannu suna rikita jijiyoyin mahaifa da ma ita mahaifar kanta, ta yadda zata dinga zubar da Jini ba gaira ba dalili, kuma a kasa shawo kan Matsalar.
Sai dai wasu kuma matan, matsalar rikicewar jinin Al'adar yana faruwa da su ne sakamakon shigar shaiɗanin aljanin nan me suna jinnul ashiƙ da yake shiga jikinsu don ya hanasu Haihuwa ko kuma aure (Duba rubutuna MATSALOLIN ALJANU DA YADDA ZA A MAGANCE SU za ku samu ƙarin bayani kan wannan Aljanin da dalilan da yasa suke shiga jikin mata da maza)
Wannan Aljani yakan je mahaifar mace ya sami wannan jijiyar da take guntsar Jini, sai yayi ta dukan/ko matsa jijiyar mahaifar, ta yadda Jini zai dinga wasa ko ma yayi ta zuba ba gaira ba dalili, ko kuma ya toshe jijiyar mahaifar ta yadda mace baza ma ta yi jinin al'adar bama ballantana har ta kai ga sake ƙwai (egg's producing) ballantana kuma Uwa Uba haihuwa.
Akwai rikicewar jinin Al'ada da yake da nasaba da sihiri, ta yadda za a je gun wani boka ko malami marar Aƙidah ta gari, sai a bashi sunan mace yayi laya sai Su je Su binne a kwata (slaughter) yadda gun bai rabuwa da Jini, to haka zata dinga zubar da jini kullum.
*MAGANIN WANNAN MATSALAR ITACE:*
1. Ki nemi ingantaccen furen Albabunaj,
2. Ganyen Sazabu
Sai ki haɗa su gu ɗaya, Sai ki dinga dafawa kaɗan-kaɗan kina sa zuma mai kyau a ciki kaman shayi kina sha safe da yamma.
Sai dai in baki samu ganyen Sazabun ba to ki yi amfani da furen Albabunaj kaɗai. Amfanin shi ganyen Sazabun shi ne; in case ko da Matsalar tana da nasaba da shigar shaiɗanin aljanin nan jinnul Ashiƙ ko kuma sihiri to in aka haɗa da ganyen sazabun zai taimaka sosai da yardar Allah.
In Sha Allahu Indai Matsalar RIKICEWAR jinin Al'ada ne, ki jarraba za ki dace da yardar Allah subhanahu wata'ala.
Babu lafi kuyi shere Domin mafi alkhairin alumma shine Wanda ya amfanar dasu.
#Azare #Gombe #Bauchi #Misau #healthy #Adamawa #nigeria #kano #Nasrawa #gwarimpa #asokoro #maiduguri #yobe #gombe #maiduguri #abuja #bauchi #suleja #nigerminna #jos #kaduna #sokoto #zamfara #health #asokoro #gwagwalada #bwari #maraba
Comments