AMFANIN HABBATUR RASHAD
Sunan sa *Habbatus Rashad* (الحبة الرشاد), ko Halim Seed, ko Aliv Seed, Garden Cress seed.
*Habbatur Rashad* wasu ƴan kwayoyi ne kanana masu kama da Habbatus sauda, sai dai su jajaye ne sannan tana da yauƙi a baki.
Wasu suna kiran Habbatur Rashad da suna *Jar Habba*
'Ya'yan *Habbatur Rashad* na da matukar mahimmanci a jikin Ɗan Adam domin yana warkar da cututtuka da dama a jikin Ɗan Adam.
Akan haɗa ƴaƴan Habbatur Rashad a cikin abinci kamar shinkafa, faten dankali, faten tsaki da kuma sauran su domin taimaka wa jiki da lafiyar mutum, amma wasu masanan sun ce, ganyen ya fi amfani a jikin mutum idan aka ci shi ɗanye, wato a kwaɗa shi ko da dakakken ƙuli-ƙuli da kayan miya.
Masanan sun bayyana irin amfanin da *Habbur Rashad* ke yi a jikin mutum kamar haka;
1. *Habbatur Rashad na maganin cutar ido*:
Habbatur Rashad na da sinadarin dake maganin cututtukan da ke kama ido.
Cin sa na da matuƙar amfanimfani.
2. Yana maganin cutar hawan jini.
3. Cin Habbatur Rashad na gyara fatar mutum.
Habbatur Rashad na maganin Kyasfi dake kama fata.
Ana niƙa shi a haɗa da man da ake shafawa ko kuma da ruwa a shafa a jiki. Yana gyara fata sosai.
4. Yana taimaka wa mutum cin abinci yadda ya kamata.
5. Yana maganin ciwon ciki kamar su zawo da sauransu.
6. Habbatur Rashad na kawar da ciwon zuciya.
7. Yana hana amai.
Idan mutum yana yawan jin amai, Habbur Rashad na maganin wannan.
8. Yana ƙara ƙarfin ƙashi.
9. Yana ƙara ƙarfin namiji.
10. Cin Habbatur Rashad na kawar da warin baki.
11. Cinsa na kawar da laulayin da mata kan ji idan suna jinin al’ada.
12. Yana rage ƙiba a jiki.
13. Yana warkar da rauni ko ciwo a jikin mutum.
14. Yana kawar da cutar siga.
15. Yana ƙara jini.
16. Amfani da Habbur Rashad yana maganin matsalar jinnu.
Don samun *Habbatur Rashad* za a iya tuntuban mu.
Fuad Islamic Medicine Misau.
No. 2. Tamsuguri Street Misau, Bauchi State Nigeria.
09031562132
08067676223
08024508141
Comments