MATSALOLIN ALJANU DA YADDA ZA A MAGANCE SU.


Rubutawa: 
Muhammad Muhammad Albani Misau

Jan hankali:

(Nine asalin mai rubutun duk wanda ka ga ya saka rubutun nan a shafi na ko a wani waje to a waje na ya ɗauka, don naga da yawa sun canza abubuwa da dama daga rubutu , don haka ina jan hankalin su da su ji tsoron Allah , su sani ilimi amana ne)
Albani Misau.




Gabatarwa:

Dukkan godiya da yabo su tabbta ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa har ya zuwa ranar tashin alkiyama.

Bayan haka wannan sako ne na musamman zuwa ga ‘yan uwa musulmai maza da mata dangane da matsalolin Aljannu da suka shafi matan aure da ‘yan mata musulmai da samari marasa aure da magidanta baki daya, dangane da matsalar shafar Aljanu, da yadda suke shiga jikin mutum dan Adam, da alamomin da dan Adam zai gane cewa akwai Aljanin a jikinsa, sa’annan bayani game da matsalar da ake kira (jinnul ashik) namijin dare ko (jinnu ashika) macen dare.
Allah na ke roko ya mun dace wajen wannan rubutun amen.

SU WAYE ALJANU KUMA DAGA INA ALLAH YA HALICCE SU?.


Aljanu halittu ne da Allah (SWA) ya yahaliccesu ya ajiye su a duniya don su bauta masa.
Sa’annan ya halicce su ne daga harshen wuta, Allah (SWA) yana cewa :
“KUMA YA HALICCI ALJANI DAGA WUTA (Harsashen Wuta)”.

Ɗan Abbas ya ce: ”Lallai Aljannu an halicce su daga harshen wuta".

Don haka sai muce Aljanu wasu halittu ne da Allah ya halicce su daga harshen wuta, shi yasa ba a iya ganin su, kuma ba a iya taɓa su ko jin motsinsu, saboda su ruhine kawai, basu da tabbataccen gangan jiki irin na ɗan Adam, shi yasa suke shiga sura irin jikin da suka ga dama, kamar Kare, Maciji, Kyanwa (Mage), da sauransu.

 NAU’IN HALITTUN ALJANU.

Allah (SWA) ya halicci Aljanu da nau’in halitta mabambanta.
An samo Hadisi daga Aba Sa’alabatal Kushaniy (RA) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce: “ALJANU NAU’I UKU NE, (Wasu) NAU’IN MASU FIKA-FIKAI NE, SUNA TASHI SAMA, DA NAU’IN MASU ZAMA MACIZAI DA KUNAMAI DA MASU ZAMA WURI ƊAYA SU ƘAURA”.
 Hakim ya fidda shi.

WURAREN DA ALJANU SUKE ZAMA.

Aljannu Sun kasance suna zama a cikin waɗannan wuraren kamar haka:-

1. Cikin Daji.
2. Cikin Ruwa.
3. Tsaunuka, da Koguna.
4. . Bayan Daki (Toilet)
5. Bola (Jibji).
6. Wajen Wanke – Wanke.
7. Wurin Makabarta.
Masu zama a cikin jama’a sun fi cutar da jama’a, saboda suna zama a wuraren ƙazanta, shi yasa mafi yawan cutarwar da Aljannu ke yi wa ɗan Adam sune suke yi!! (Allah ya tsare mu).

DALILIN DA YASA ALJANU KE SHAFAR ƊAN ADAM.

Yawancin Aljannu suna shafar ɗan Adam ne ta ɗaya daga cikin waɗannan dalilai guda 4:-

1. Saboda zalunci da muguntar Aljanin.

2. Da sunan kauna ko son da Aljani ke yi wa dan Adam, kamar Aljani ya so mace mutum, ko Aljana ta so namiji mutum.
A gaba za mu yi bayani akan wannan matsalar, kuma shi ake kira da Jinnul Ashiƙ (Namijin Dare) ko Jinnul Ashiƙa (Macen Dare) insha Allahu.

3. Saboda cutarwar da ɗan Adam ya yi wa Aljanun, kamar ya zuba masa rowan zafi ko ya taka shi, sai ya zo ɗaukar fansa.

4. Ko Bokaye da matsafa su turo wa mutum Aljanin.

CUTARWAR DA ALJANI KE YI WA ƊAN ADAM.

Aljanu na cutar da ɗan Adam ta hanyoyi guda 2, kamar haka:-

1. Ta hanyar shiga jikin ɗan Adam:- Shine Aljani ya shiga jikin ɗan Adam gaba daya ko wata gaba, kamar hannu, kafa, Baya, Kirji, Kai, Ido ko Kunne, sai yayi ta cutar da marar lafiya yana wahalar dashi.
Wannan ya tabbata a cikin Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya ce:
“LALLAI SHAIƊAN (ALJANI) YANA GUDANA A JIKIN ƊAN ADAM AKAMAR YADDA JINI YAKE GUDANA”.
Ma’ana: Yana iya shiga duk inda jini zai shiga, saboda bashi da gangan jiki da zai hana shi hakan.

2. Ta hanyar Shafar jikin ɗan Adam:- Shine ya sanya masa ciwo ko kuma ya lalata wata gaɓa daga cikin gaɓoɓin jikin ɗan Adam, kamar ya lalata ko shanye hannu, ya sanya ciwo, ko ya kurumtar da kunne, ko ya rike muryar mutum, ko ya sanya wa mace ciwo a mara, ko mahaifa, ko ya taɓa mata wata jijiya sai jini ya yi ta zuba, da-dai sauransu.
Irin waɗannan Aljanun ba a samunsa a jikin marar lafiya, sai dai ayi ta amfani da magani wanda musulunci yayi umurnin amfani dashi, ta kuma hanya mai kyau.

LOKOTAN DA ALJANI KE SHIGA JIKIN ƊAN ADAM.

1. Yayin da mutum yake cikin matsanancin bacin rai da fushi.
2. Yayin da mutum ya tsorata.
3. Yayin da Mutum ya nitse cikin sabon Allah, kamar kallace-kallacen fina-finan banza na batsa.
4. Yayin da mutum yaje ya kama yawo acikin janaba, saboda babu garkuwa na tsarki a jikinsa.

ALAMOMIN SAMUWAR A JIKIN DAN ADAM.
1. Yawan mantuwa mai tsanani.
2. Mutuwar wani bangare
na jiki, hannu ko kafa wanda baya jin magani.
3. Yawan samun damuwa da kuncin rai.
4. Rashin natsuwa a guri daya.
5. Yawan kokwanto.(Rashin tabbas)
6. Firgita a cikin barci.
7. Yawan mafarkin matattu.
8. Yawan mafarkin jini ko ruwa.
9. Mafarkin maciji.
10.Jin motsi kamar ana binka a baya.
11. Cizon hakori a cikin barci.
12. Yawan rashin bacci.
13. Yawan farkawa daga bacci.
14. Mafarkin Shanu.
15. Mafarkin saduwa (Jima’i) ba bisa ka’ida ba, kamar sau 3 fiye da haka a sati.
16. Yawan zubar jinin haila wanda ya wuce misali.
17. Yawan zancen zuci.
18. Rashin amincewa da mutane.
19. Yawan faduwar gaba.
20. Tafiya ko tsayuwa a cikin bacci.
21. Yawan mafarkin abubuwan ban tsoro.
22. Yawan yawace yawace ba bisa qa;ida ba. Kawai mutum yaji bai ita zama wuri daya.
23. Yawan jin tsoro haka kurum.
24. Yawan Rashin jituwa tsakanin miji da mata.
25. Jin sauti kamar ana kiranka.
26. Dadewa a bandaki ba tare da wani dalili ba.
27. Zancen zuci a bandaki.28. Mafarkin kyanwa (mage). Da sauransu.

Da zaran dan Adam ya ji wannan alamomin a jikinsa, to akwai alamar samuwar aljani a tattare dashi, sai ya fara addu’a da yawan azkar, da yawaita karatun alku’ani.
Idan kuma ya fara jin ciwon kai, ciwon kirji, ciwon baya, ko ciwon gabobi, bayan wadancan alamomi da suke sama, sai ya ci gaba da addu’a tare da shan magani, in kuma abun yayi tsanani, sai ya nemi Malamim Ruqiyya (Ahlus Sunnah), su yi masa, karatun Alkur’ani. Allah ya tsare mu.

ABINDA AKE KIRA JINNUL ASHIK:-

Shi ne mace ta wayi gari tana yawan mafarki wani na saduwa da ita cikin barci, wannan al’amarin ya kasance ya yi yawa a tsakanin mata kuma har ya kai ga wasu cututtuka suna faruwa ga mace ko namiji ko kuma cututtukan da ba sa jin magani a yi ta wahala har a gaji.

DALILIN SAMUWAR JINNUL ASHIK:-
Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alqur’ani da Sunnah, kamar cikin Majmu’ul fatawa na Shaikul Islam ibnu Taimiyyah da littafin Ash-shifa’u bil qur’an minal jinnu washshayadini na Ridha Ash-sharkawi da littafin Minhajul qur’an li’ilaj as-hir wal massi as-shaidani suka ce:
Wannan Aljani da ake kira jinnul Ashik yakan samu mace ta hanyoyi hudu kamar haka:-

<1>: Wata shi yake kawo kansa saboda rashin kyautata sutura da shigar banza na kayan zamani, wanda musulunci ya hana.
. <2>: Wata kuma ita take kai kanta inda aljanun suke, kamar zuwa wajen bokaye.
<3>: Wata kuma sihiri aka yi mata saboda ta hada nema da wani maras tsoron Allah.
<4>: Wata kuma tana kyautata sutura, tana bin Allah, amma Allah zai jarrabe ta da wannan shaidani.
A takaice dai wadannan hanyoyin da shi wannan shaidani zai zo wajen ta sai ya mayar da abin ya koma zuwa soyayya ya raba ta da kowa ya hanata yin aure ko ya rabata da mijinta ko ya hanata zaman lafiya da shi, shi kuma Aljanin ya ci gaba da zama da ita yana saduwa da ita ya dauke ta kamar matarsa kuma ya hana mijinta komai da ita, ya sa gaba da kiyayya a tsakaninsu. Allah ya kiyayemu..

*HANYOYIN DA YAKE BI YA ZO MATA A MATSAYIN MIJIN DARE.*

SUNE KAMAR HAKA:-
<1>: Yakan zo wa macce cikin barci ya dinga saduwa (jima’i) da ita cikin mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wadda take jin kunya ko wanda bata sani ba ko dan uwanta ko ta siffar mace ‘yar uwarta.
<2>: Yakan zo mata a siffar mijinta yana saduwa da ita a zahiri ba a mafarki ba, amma kuma shaidani ne ba mijinta ba ne.
<3>: Yakan zo wa mace tana kwance ta ji kamar ana saduwa da ita, ita ba mafarki ba, ita kuma ba idon ta biyu ba.
<4>: Wata macen ta kan kwanta ta yi barci ba wanda ya sadu da ita, amma idan ta farka ta wayi gari sai ta ga kamar wani ya sadu da ita.

*ALAMOMIN MIJIN DARE:-*(JINNUL ASHIQ)

👇

👇

👇

👇

👇

👇
Daga cikin alamomin da macce zata gane tana da wannan matsalar shine:-
Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita cikin barci, yawanci mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayin, amma sai su dauka shirmen mafarki ne kawai, to a gaskiya ba haka bane. Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin za ka same ta tana fama da wadannan matsalolin, ko da za ka tambaye ta wadannan matsalolin za tace maka tana fama da su. Daga ciki akwai:-
<1>: Bacin rai ba a mata komai ba, ta ji tana jin haushin kowa har ma da mijinta ko kuma ta ji kamar mijin ya sake ta, ta gaji da auren, da za ka tambayeta laifin mijin ba zata fadi laifinsa ba, wata rana ma ta ji tana tsanar ‘ya’yanta.
<2>: Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma baya jin magani.
<3>: Tsananin ciwon kirji da ciwon baya.
<4>: Tsananin ciwon mara lokacin al’ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin macce, shi ba al’ada ba ne, kuma ya kasu kashi 2; mai yauki da maras yauki ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi ko fitowar kuraje.
<5>: Ga yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun ciki, amma za ta iya kasancewa ta dauki alamomi na masu ciki har ma ana zaton tana da ciki, amma ana kwana 2 sai ta canza kamar ba ciki ba, ko ta rinka yawan mafarkin ta haihu.
<6>: Idan mijinta yana saduwa da ita tana jin zafi, ko kuma yana saduwa da ita ba zafi, amma bata samun biyan bukata.
<7>: Daf da magariba ta dinga jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawan tsorata, ko kasala da bacin rai.
<8>: Idan ta dauki Alkur’ani za ta karanta sai ta dinga jin kasala da hamma da hawaye da barci da zarar ta ajiye kur’anin sai ta ji tawartsake kamar ba ita take jin barci ba.
<9>: Sannan kuma ko ta kwanta tana son yin barci sai ta kasa, ta yi ta juyi ta kasa barci, mijinta na zuwa kusa da ita sai ta dinga samun firgita da tsoro.
<10>: Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga kadewa ko ya yi ja, bakinta ya dinga bushewa ko yayi ja.
<11>: Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani, amma ba amosani ba ne.
<12>: Yawan kaikayin kunne da yawan kaikayin hanci kamar mura, amma ba mura bane, ko yawan kunburin ciki.
<13>: Yawan zuban jini daba na al’ada ba, ko jini ya rika yi mata wasa.
Sannan kuma har ma wacce bata da aure budurwa ko bazawara za ta iya samun wannan matsalar, amma ita bambancin da ke tsakani da ita wacce take da aure shine kamar haka:-
<1>Ita marar aure za ta kasance duk lokacin da wani ya zo wajen ta da maganar aure kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga wajensa.
<2>Za ta dinga samun munanan mafarkai tare da ganin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita cikin barci ta fuskar da ta sani ko bakuwar fuska ko mace ‘yar uwarta.
<3>Kuma za ta dinga yawan samun cututtuka masu wuyar magani har ma da yawan zubar da jini ko ciwon mara lokacin al’ada ko kasala lokacin karatun kur’ani, tana farawa sai hamma da kasala ya kama ta ko kuma idan ana sallama da ita, sai ta rinka jin faduwar gaba ko tsoro.
<4>Kuma za ta rinka yawan samun sabani da kiyayya tsakaninta da iyayenta ko ‘yan uwanta ko jama’a ko kuma ta zama mai rashin kunya da rashin jin magana ga iyaye da sauran dangi.
Allah ya kiyaye.

*GAME DA NAMIJI:*
Dukkan wadannan bayanai da aka yi game da ‘yan uwa mata, to sukan iya samun da namiji, amma bambanci shine:-
Shi namiji macen Aljana ce za ta dinga zuwa wajensa ta zama ta raba shi da kowa sai ita kadai, ta dauke shi kamar mijinta, idan mai mata ne ta cire soyayya da sha’awa tsakaninsa da matarsa, kuma ta hana shi komai na ci gaban rayuwarsu, ta mayar da shi marar kishin kansa da rayuwarsa.
Idan saurayi ne takan hana shi karatu ko ya fara ba zai gane ba, ko kuma inya gane ta hana shi karatun ko ta dinga sa masa wasuwasi da kokwanto lokacin jarrabawa ya fadi ko a kore shi a makarantar, in ya kama neman aure ko a ki shi ko shi ya ki, in ya kama sana’a sai ya yi ta samun matsala, kuma shi ba shan Giya, ko mata yake nema ba, kuma tasa gaba da rashin yarda tsakaninsa da iyayensa ko jama’a.

MAFITA GAME DA ALJANNU.

Duk wadannan abubuwa da aka fada ba abubuwa ne sabbi ko baki ba, ba kuma yau ko jiya aka fara samun wannan matsalar ba, wannan matsalar an same ta tun zamanin Annabi (SAW) game da Aljani ko Aljana ya shiga jikin dan Adam namiji ko mace.
Imam Bukhari ya ruwaito hadisi zamanin Annabi (SAW) an samu wata mace tazo gaban Annabi da matsalar cutar Aljani yana kayar da ita, ta fadi, ta ce Annabi ya yi mata magani.
Sai Annabi (SAW) yace” mata, da a barki da cutarki kimutu ki shiga aljannah, da a yi miki addu’a ki warke wanne ki ka fi so?! Ta cewa Annabi (SAW) idan wannan cutar za ta zama sanadin shigata Aljannah, a barta da shi, amma ayi mata addu’a idan ya kada ita, ta dai na tsiraici.
Don haka wannan al’amari ba bako bane ga musulmi ko Ahlus Sunnah.
Komawa zuwa ga Allah (SWA) da kuma rike addu’o’in da Manzon Allah (SAW) ya ba muna safe, yamma da na shiga ban daki da fita, da na lokacin kwanciya, da na sanya sutura da cirewa, da na cin abinci, duk wadannan suna cikin littafin (HISNUL MUSLIM), sannan kuma sai wadannan hanyoyin da Malami suka bayar guda 11, ga me da mace ko namijin da suka samu kansu da namijin dare ko macen dare:
1. Su kiyaye dokan Allah (SWA) da nisantar laifuka manya da kanana.
2. Yawaita karatun Kur’ani a kawane hali a kuma kowane lokaci.
3. Kyautata sutura (mace) hijabi, tin daga sama har kasa, mai kauri kuma mai fadi bana adoba.
4. kiyaye cin halal wanda za a ci ko wanda za a nema.
5. Yin sallah akan lokaci tare da kiyaye ilmin sallah din tun daga Annabi (SAW).
6. Yawan yin Alwala lokacin da za a kwanta bacci da kowane lokaci.
7. Yawan karanta Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasulu, kulhuwa, Falaqi da Nasi lokacin kwanciya.
8. Yawan karanta Suratul Baqara a gida ko dakin da ake kwana da cire hoto ko na waye.
9. Yawan Karanta:- LA’ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA HUWA ALA KULLI SHAI’IN QADIR. Sau 100 da safe da yamma.
10. Karanta BISMILLAHIL LAZI LA YADHURRU MA’A ISMIHI SHAI’UN FIL ARDHI WA LA FIS SAMA’I, WA HUWAS SAMI’UL ALIM. Sau 3 da safe da yammaa.
11. Da Karanta: A’UZU BIKALIMATILLAHIT TAMMATI MIN SHARRI MA KHALAK. Sau 3 safe da yamma.

HANYA TA BIYU. Game da wadanda suka tsinci kansu cikin wannan matsalar, ta jinnul Ashik, za ta samu tsabar habbatus Sauda, sai ta karanta Suratul Baqara gaba daya a cikin wannan tsabar, sai a dinga hayaki a dakin da take kwana, kuma sai ta tsuguna kan hayakin ya dinga shiga jikinta, za ta rinka yin haka da safe da lokacin da lokacin kwanciya.
Sai kuma amfani da magungunan Islama wadanda musulunci ya karantar ayi amfani dasu.
Wadannan ba zan bayyana su anan ba, duk wanda yake buƙatar maganin sai ya tunbuɓe ni.

Alhamdulillahi Ala kulli Haal!!

Muhammad Muhammad (Albani) Misau.
 
+2348067676223
+2349031562132
+2348024508141

Comments

Popular posts from this blog

WASWASI (KOKONTO) [DEPRESSION] DA KUMA HANYOYIN WARWARE SHI

AMFANIN SHAMMAR GA MATA TA ƁANGAREN NONO

BRAIN BOOSTER