Maganin ciwon kai mai tsanani, ko na gefe ɗaya.
Daga *Fuad Islamic Herbal Medicine Misau*
https://www.facebook.com/1844052855851575/posts/3150592095197638/
_Shin kana fama da matsalar jujuyar kai, wanda yake yawan maimaituwa, wanda yake haddasa ciwon kai mai raɗaɗi?_•
_To ga hanyar da za ka bi ya kai ɗan uwa ƴar uwa, domin waɗannan magungunan suna taimakawa matuƙa._•
(1) Ɗanyan citta cokali ɗaya. Idan kuma busash-she ne ƙaramin cokali._
(2) Sai Kuma sarkin magunguna wato itaciyar *Iklilil jabal*, wanda a harshen turance ake Kira da (Rosemary)_
(3) Zaka samo Lavender, wanda a kira da harshen larabci cewa (Kazama)._
(4) Zaka samo Yansun._
Yadda zaka haɗa shine:
_Zaka zuba ƙaramin cokali na kowanne maganin amma banda ɗanyar citta, zaka zuba cokali ɗaya ne ita, amma kada amanta, a baya munce idan busash-she ne ƙaramin cokali, ko rabin cokali ya isa._
_Zaka tafasa ruwa sai kazuba ruwan ɗumi akai, amma wanda aka dafa sosai, bayan an zuba sai ka rufe kabar shi, bayan mintina kaɗan sai ka tace ka rinƙa shan kaɗan-kaɗan, lokaci-lokaci, insha Allahu a ƙarshe za kaga sakamako Mai Kyau._
•
_*(2)-* Amma idan wannan tayi wahala to kabi wannan bayanin ka samo_
-Ƙusdul hindi.
-Garin Habbatus sauda.
-Garin Hulba.
-Garin Hiltit.
_- Garin kanin fari._
_Bayan haka wannan yana taimakawa wajen sauƙaƙa matsalolin zuwan jinin al'ada, ko sanyin mara, ga mata, da Kuma maza._
•
_Bayan an haɗa sai a riƙa tafasa wa ana yin suracensa, ana Kuma zuba wani a ruwa wanda aka tafasa kana sha, da zuma ko madara insha Allahu wannan hanyama Za a iya samun waraka bi'iznillah._
•
_*(3)-*. SURATUL FATIHA : Malaman Musulunci sun ce lallai Fatiha ta na maganin kowacce irin cuta a jikin Ɗan Adam.
Yadda za ka yi amfani da ita domin magance matsalar ciwon kai shine:
Kayi Basmalah ka sanya hannunka na dama ka riyke goshinka ko kuma wajen da yafi ciwon.
ka karanta Fatiha ƙafa ɗaya sannan ka saki kan naka.
.In sha Allahu zaka ji ya dena._
•
_Idan bai dena ba, ka sake riƙe wa sannan ka karanta Fatiha ɗin ƙafa uku. Za ka ji ya dena.
Idan kuma bai dena ba, ka karanta ƙafa biyar, idan bai dena ba, ka karanta ƙafa bakwai.
In Allah ya yarda za ka ji ka warke nan take._
•
_*HAYAKIN HABBATUS SAUDA :*
Ka samu ƙwayoyin Habbatus Sauda ka zuba a cikin Garwashi sannan ka riƙa shaƙar hayaƙin.
In sha Allahu za kaji babu ciwon kan._
•
_*MAN TAFARNUWA, MAN GELO :*
Kowannensu idan ka shafa zaka samu waraka daga ciwon kan. Wannan ko da shaiɗanu ne suke sawa za a rabu da shi in shaaAllah._
.
```Allah ta'ala yasa mu dace```
*FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE*
No 2. Tamsuguri Turaki Street, kusavda gidan mrigayi Alhaji Ahmed Katibu Misau.
09031562132
08067676223
08024508141
Comments