CIWON CIKI DA CIWON MARA LOKACIN AL'ADA

Fuad Islamic Herbal Medicine.

Gabannin na yi bayanin kan magungunan da za a yi amfani da shi yana da kyau na bayyana muku wani ɗan bayani kan Hakika kamar haka 👇

BAYANI DANGANE DA HAILA

Ana haihuwar yara mata da wasu ƙoyaye biyu (ovaries) Waɗanda ke ƙunshe da dubban ƙoyayen da ba su nuna ba (duba shafi a kan Halittar jikin namiji da macce).

Bayan yarinya ta balaga, a kowane wata tana sakin ƙwai ɗaya da ya nuna. Ana kiran wannan ‘saukar ƙwai’ (ovulation), kuma wannan na faruwa wajejen kwana goma sha hudu kamin soma al’ada.
Idan ƙwan bai haɗu da maniyyi ba sai ya mutu.
A ko wane wata mahaifa na shirya wa yiwuwar ɗaukar ciki, kuma fata ta cikin mahaifa na zama da kauri da kuma taushi.
Idan jikin macce ya gane cewa ba maganar ɗaukar ciki, sai fatar da ke cikin mahaifa, tare da ƙwan su zama haila su fice ta al'aura.

Ba za a iya ganin ƙwan ba saboda ya cika ƙanƙanta.

Ana fara ƙirga lokacin haila daga ranar da aka fara, zuwa jajibirin ranar da za a fara wata al’adar.

Zagayowar al’ada na canzawa, don zai iya kasancewa kwana ashirin da ɗaya ko kuma ma zai iya kai wa kwana arba’in.
Idan macce na al’ada, tana iya amfani da tawalin al’ada ko kuma fad, ko audugar al’ada don ta tare jinin da ke zuba.
Kina iya yin amfani da littafin tsarin lokaci watau diary domin sanin lokacin da za ki fara al’ada.

Ba dukan mata ne ke yin al’ada a kan lokaci ba, kuma lokacin fara al’ada ya bambanta.

Wasu ƴan matan na farawa tun da wuri (Alal misali tun suna da shekara takwas), yayin da wasun ke daɗewa basu fara ba. Haka ma, tsawon lokacin da ake ɗauka ana hailar ya bambanta daga mace zuwa mace.

Yawanci suna yin kwana biyar zuwa bakwai. Amma kuma wannan na iya sauyawa, don a wasu lokutan ba a kaiwa kwana biyar.

Da zarar yarinya ta fara al’ada, zai ɗau lokaci kamin jikin ta ya saba.

A shekarar farko mai yiwuwa ta ƙetare wata ɗaya ko fiye da haka bata ga haila ba. Amma yau da gobe jikin nata zai saba.

Irin canjin da ake samu na yawan sinadarin (hormone) da jikin mace ke samarwa kamin lokacin yin al’ada, ko kuma a lokacin al’adar, mai yiwuwa ya shafi halin da mace zata nuna, ko kuma abinda zata ji a ran ta. Mai yiwuwa ta ji ƙarin kuzari, ko kuma ta ji tana sha’awar namiji, ko kuma ran ta ya ɓaci, ta ji kamar ta yi kuka, ko kuma ta riƙa yawan fushi a lokacin saukar ƙwai ko kuma jim kaɗan kamin ta fara haila. Mai yiwuwa nonunan ta su riƙa ciwo ko su ƙara girma; kuma a wasu lokutan wasu ƙananan ƙuraje kan fito a fuska.

Wasu matan sun ɗara saura jin bambam a jikinsu a lokacin da suke haila. Kuma wannan na iya sauyawa a rayuwar mace.

Ta haka ne mata ke sakin ƙwayaye har zuwa lokacin da suka daina haila.
A yawancin lokuta hakan na faruwa idan mace ta kai ƙarshen shekaru arba’in zuwa hamsin.
Bayan wannan lokacin, ba zata ƙara yin al’ada ba, kuma ba zata ɗauki ciki ba.

Idan kina matuƙar jin ciwo a lokacin al’ada, ko kuwa kina da wata damuwa, sai ki nemi shawara daga likitan da ki ka yarda da shi.

*MAGUNGUNAN DA ZA A YI AMFANI DA SHI*

Da zarar budurwa ko matar auren da take fama da wannan matsalar abinda za ta yi shine sai ta samu waɗannan magungunan kamar haka:

1. Garin Hulbah 


2. Garin Habbatus sauda


3. Garin Kiswatul Hindi (Qusdul Hindi).


Sai ki haɗa su waje ɗaya ki zuba ruwa da Zuma a ciki sannan ki dafa su idan ya dafu sai ki ajiye wannan ruwan da safe ki ɗebi ƙaramin kofi ki sha kafin ki ci komai ana so ki dafa wanda zai miki sati ɗaya kafin ya ƙare kin huta da wannan matsalar insha Allah.

FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE MISAU.

No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau opposite Alhaji Ahmed Katibu Misau House.

+2349031562132
+2348067676223
+2348024508141

Comments

Popular posts from this blog

WASWASI (KOKONTO) [DEPRESSION] DA KUMA HANYOYIN WARWARE SHI

AMFANIN SHAMMAR GA MATA TA ƁANGAREN NONO

BRAIN BOOSTER