DOMIN SAMUN GARKUWAR JIKI
FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE MISAU.
Wannan haɗin yana da matuƙar muhimmanci musamman a wannan lokacin da mu ke ciki, domin zai ƙarfafa wa mutum garkuwar jikin sa ya kuma kare shi daga dukkan wata cuta.
haɗa waɗannan abubuwa kamar haka;
1. Koren Ganyen Shayi (Green tea).
2. Garin Habba (Black Sead).
3. Kanan Fari (Clove).
4. Ƙirfa (Cinnamon).
5. Citta (Ginger).
6. Ciyawar Lemon (Lemon Grass).
7. Na'ana (Pepper Mint).
*YADDA ZA A YI AMFANI DA SHI.*
A haɗa su waje ɗaya, sai a tafasa kamar yadda ake yin shayi, sai a haɗa da zuma idan za a sha, a matsa rabin lemon tsami (Lemon juice) ko a hada lemon tsamin gaba daya a tafasa wuri guda.
Sai a rinƙa sha safe da yamma.
Allah ya mana dace amin.
Fuad Islamic Herbal Medicine Misau.
No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau.
+2348067676223
+2349031562132
#Fuad_islamic_medicine_misau
Comments