AMFANIN SHAYIN GORIBA A JIKIN ƊAN ADAM

Tambaya:
Malam muna son mu san amfanin goriba musamman da a yanzu ake yin shayin ta kuma ana ba shi muhimmanci har a kantuna ana sayar da ita.

Amsa:
Goriba wata bishiya ce da ta daɗe a duniya, amma an fi samun ta a ƙasashen Afrika, saboda tana da juriya na yanayi.
 Sunan ta da Turanci ‘Doum Palm Tree’. 
Ta na ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya ɗan Adam.
 Don haka ake amfani da ita wurin inganta lafiya da yin kariya ga wasu cututtuka da kan addabi ɗan Adam.


 Daga cikin amfanin goriba akwai:-

•Ta na magance matsalolin jiri yayin da aka tafasa ta aka sha ruwan musamman a haɗa da garin Habbatus Sauda a tafasa su tare asha.

*Ga namiji mai rauni, yawaita shan shayin goriba zai magance wannan matsalar.
 Haka kuma ana iya shaƙar ƙwallon ta a riƙa sansana shi ko kuma a ƙone ta a riƙa shaƙar ƙwallon duk yadda aka yi yana magance matsalar jiri.

•Haka ga mai larurar hawan jini shan tafasasshen ruwan goriba, amma a bar shi ya huce ba da zafi za a sha ba zai daidaita hawan jini.

•Goruba tana magance matsalar basur sosai idan aka tafasa ta da ɓawon ta aka sha ruwan.

•Ga waɗanda ke da yawan kitse a jiki ko ƙiba shan shayin goriba yana dai-daita shi da ikon Allah.
•Sannan ga mai jin nauyin jiki shi ma duk ana amfani da ruwan goriba ko kuma garin. 
Sai dai a tabbatar mai tsafta ne an wanke shi yadda ya kamata, saboda sau tari mutane da sun karɓo a kasuwa sai su hau ci ba tare da la’akari da tsaftar ta ba. 
Don haka muka riƙa cewa a tafasa sai ta fi inganci sannan a sha.
 
•Masu larurorin fitsari goriba tana kawo sauƙi.

•Ga wanda yake fama da yawan gajiya ya lizimci shan shayin goriba ko lemun ta zai samu kuzari insha Allahu.

•Goruba na yin maganin cushewar ciki shi ma a tafasa a sha ko kuma a yi lemon ta.

•Lizamtar shan shayin goriba ko lemon ta yana rage damuwa irin wadda kan zo wa mutum ko da dalili ko babu kawai sai mutum ya tsinci kan sa ko dai cikin damuwa ko ma ya ji yana jin haushin kowa.

Fuad Islamic Herbal Medicine.

No 2 Tamsuguri Turaki Street Misau, Bauchi State Nigeria.

+2349031562132

Comments

Popular posts from this blog

WASWASI (KOKONTO) [DEPRESSION] DA KUMA HANYOYIN WARWARE SHI

AMFANIN SHAMMAR GA MATA TA ƁANGAREN NONO

BRAIN BOOSTER