Posts

Showing posts from March, 2022

DOMIN NARKAR DA TSAKUWAR MARA

Fuad Islamic Medicine Misau A samu: * Hulba cokali biyar. * Shammar cokali uku. * Badunas cokali biyu. * Garin Habba cokali biyar. Yadda za a yi amfani da shi:  A haɗa su wuri ɗaya, sai a rinƙa ɗiban cokali ɗaya da ruwa kofi ɗaya ana dafa shi, bayan ya dahu sai a ɗebi cokali biyu a shanye, haka za a rinƙa yi safe kafin a karya, da kuma da daddare kafin kwanciya bacci. Insha Allahu za a ga abun mamaki. Allah ya taimaka. Fuad Islamic Herbal Medicine Misau No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau, kusa da gidan Marigayi Alhaji Ahmed Katibu Misau +2348067676223  +2349026250922.

DOMIN SAMUN GARKUWAR JIKI

Image
FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE MISAU.        Wannan haɗin yana da matuƙar muhimmanci musamman a wannan lokacin da mu ke ciki, domin zai ƙarfafa wa mutum garkuwar jikin sa ya kuma kare shi daga dukkan wata cuta.   haɗa waɗannan abubuwa kamar haka;           1. Koren Ganyen Shayi (Green tea). 2. Garin Habba (Black Sead).          3. Kanan Fari (Clove). 4. Ƙirfa (Cinnamon). 5. Citta (Ginger). 6. Ciyawar Lemon (Lemon Grass).   7. Na'ana (Pepper Mint).          * YADDA ZA A YI AMFANI DA SHI. *      A haɗa su waje ɗaya, sai a tafasa kamar yadda ake yin shayi, sai a haɗa da zuma idan za a sha, a matsa rabin lemon tsami (Lemon juice) ko a hada lemon tsamin gaba daya a tafasa wuri guda. Sai a rinƙa sha safe da yamma.   ...

AMFANIN SHAMMAR GA MATA TA ƁANGAREN NONO

Image
AMFANIN SHAMMAR GA MATA Fuad Islamic Herbal Medicine Misau. Haƙiƙa gaskiya ne nono ado ne a wajen mata, domin rashinsa ko ƙanƙancinsa tawayane a wajensu, kuma maganan gaskiya sunfi jan hankalin mazajensu idan mace tana da shi dai dai gorgodon hali. Saboda haka nakeso ƴan uwa mata ku mayar da hankali ku fahimci wannan bayani sosai. Gyaran nono a wajen mace ya kasu kashi uku: Na farko: - Rashinsa ko kyankancinsa tana so ya ƙara girma. Na biyu kuma: - Girmansa ya yi yawa sosai tana so ta rage shi ya koma madaidaici saboda girman yasa nonon har ya zube kamar mai shekaru Arba'in gata kuma shekarunta kaɗan, ko kuma budurwace ma bata taɓayin aure ba gashi har nononta ya zube. Na uku kuma: - Ya kwanta gaba daya tana so ya miƙo ya koma kamar ta ƴar budurwa ƴar  sha bakwai. To lalle ku sani kowanne daga cikinsu waɗannan kashin da muka kawo akwai abubuwa da za a yi amfani da su kuma a samu biyan buƙata cikin sauƙi, don na kula yawancin mata suna da ƙishir ruwan irin w...

MAGANIN FIBROID DA IZININ ALLAH

Image
FUAD ISLAMIC HERBAL MEDICINE MISAU. MECECE FIBROID : Fibroisis wata irin nau'in chutar daji ce dake tsirowa a cikin mahaifar mace kuma tana haddasa manyan matsaloli ga mace. Musamman ta ɓangaren rikicewar jinin al'adarta, zubar jini marar misali, kumburin mahaifa da kuma rashin samun haihuwa. MINENE ABINYI : Duk da cewa yana da wahalar magani a likitancin Bature har sai anyi aiki an yankeshi (watakil kuma ya sake tsirowa daga baya) to amma a likitancin Musulunci akwai wani haɗi na musamman da ake yi domin magance shi baki ɗaya INSHA ALLAH. Haɗin kala-kala ne kuma akwai waɗanda mun jarrabasu akan marassa lafiya da dama kuma anyi an dace.  Ga wani nan kamar haka : *KI NEMI : Shajaratu Maryam ki jiƙa kina sha kina chanja saiwar duk bayan kwanaki 3 har sai kinyi sati biyu kina sha. Kuma zaki nemo : _- Garin Habbatus Sauda._ _- Garin Hulbah._ _- Garin Habbatur Rashad._ A samu Gwangwani 2 na kowanne daga cikinsu, a haɗa waje guda tare da Gwangwani 4 na garin Hiltit. * YA...

CIWON CIKI DA CIWON MARA LOKACIN AL'ADA

Image
Fuad Islamic Herbal Medicine. Gabannin na yi bayanin kan magungunan da za a yi amfani da shi yana da kyau na bayyana muku wani ɗan bayani kan Hakika kamar haka 👇 BAYANI DANGANE DA HAILA Ana haihuwar yara mata da wasu ƙoyaye biyu (ovaries) Waɗanda ke ƙunshe da dubban ƙoyayen da ba su nuna ba (duba shafi a kan Halittar jikin namiji da macce). Bayan yarinya ta balaga, a kowane wata tana sakin ƙwai ɗaya da ya nuna. Ana kiran wannan ‘saukar ƙwai’ (ovulation), kuma wannan na faruwa wajejen kwana goma sha hudu kamin soma al’ada. Idan ƙwan bai haɗu da maniyyi ba sai ya mutu. A ko wane wata mahaifa na shirya wa yiwuwar ɗaukar ciki, kuma fata ta cikin mahaifa na zama da kauri da kuma taushi. Idan jikin macce ya gane cewa ba maganar ɗaukar ciki, sai fatar da ke cikin mahaifa, tare da ƙwan su zama haila su fice ta al'aura. Ba za a iya ganin ƙwan ba saboda ya cika ƙanƙanta. Ana fara ƙirga lokacin haila daga ranar da aka fara, zuwa jajibirin ranar da za a fara wata al’adar. Zagayowar...