Posts

BRAIN BOOSTER

Image
*Brain Booster.* ************************* Ku rubuta ku ajiye saboda maganin wata rana! Ana buƙatar samun: * kuzama (lavender). * Garin Shammar.  * Garin Na'ana.  * Arar.  * Garin irƙus Sus.  Su za a niƙa a haɗa su a wuri ɗaya a rinƙa sha a ruwan shayi da madara, ko kuma da Zuma.  Wannan haɗin itatuwan yana taimakawa wajen;  ✓ ƙara fahimta. ✓ Yana ƙara kaifin hadda.  ✓ Yana taimakawa wajen saukaika wahalar karatu.  ✓ Yana sanya ƙwaƙwalwa ta wartsaƙe.  ✓ Yana ƙarfafa ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa.  ✓ Yana sauƙaƙa yawan tunane tunane.  ✓ Yana taimakawa bangaren yawan damuwa.  ✓ Da sauran matsalolin da suka shafi ƙwaƙwalwa.  Ka na iya taimaka ma yaranka da wannan/ki na iya taimaka wa yaranki da wannan.  Muna da haɗaɗɗen maganin ga wanda yake buƙatar sa.  Za a iya tuntubar mu a  +2349031562132 +2348067676223 Za a iya samun sa kuma a kuɗi kaɗan in Sha Alla...

MAGUNGUNAN MUSULUNCI.

Image
*MAGUNGUNAN MUSULUNCI.* Fuad Islamic Herbal Medicine Misau MAGANI A SAUƘAƘE in Allaah Yaso ▪Garin Habba  ▪Man Habba  ▪Man Zaitun  ▪Man Hulba  ▪Farin Zuma A haɗa su waje ɗaya, Kullum daga safe mutum yana Sha, kafin ya karya, in yazo kwanciya ma ya Sha.         Malamai suka ce sunanta *" Ash-Shifa '"* duk wata cuta da take jikin ɗan Adam tana warkar da shi... Da izinin Allaah.......  Dalili suka ce duk icen da aka faɗa a wajen,  sai da Manzon Allaah SAW ya ambace su a matsayin magani........  🕋 Manzon Allaah SAW ya ce: 🍃 HABBA waraka ce daga ko wacce cuta, banda Mutuwa da Tsufa.  🌳 ZAITUN ya ce: Ku ci ƴaƴan ku shafa man Akwai albarka a ciki.  🍯 ZUMA, alƙur'ani ya ce: Akwai abinda ke warkar da ɗan Adam a cikin ta.  🍃 HULBA ya ce: Ku riƙeta a matsayin magani Idan cuta ta sameku.....  🌐 Shafin mu a yanar Facebook: https://m.facebook.com/fuadislamic...

AMFANIN MAN ZAITUN GA ƊAN ADAM

Image
Da sunan Allah mai yawan Rahmah mai yawan jin ƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaba, farin jakada, Annabi Muhammad Sallallāhu alayhi wa Sallam da Ahalin  gidan sa zaɓaɓɓu da sahabban sa masu girma baki ɗaya. *ZAITUN DA MAN ZAITUN* Haƙiƙa zaitun itaciya ce mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin ɗan Adam, kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayanin ta a cikin Littafin Allah mai Tsarki (Alƙur'ani), haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam. An samu daga sayyadina Umar Allah ya ƙara masa yarda yana ce wa:  Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam ya ce:  *"Kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafa shi a jikin ku, domin haƙiƙa shi yana daga cikin bishiya mai albarka.* Tirmizhy ne ya ruwaito shi. *KAƊAN  DAGA CIKIN AIKIN DA ZAITUN YAKE YI GA LAFIYA SUN HAƊA DA:* ́ 1. *ƘARFIN MAZAKUTA* Duk mutumin da ya samu kan shi a wannan hali, to ya samu garin habbatus...

DOMIN NARKAR DA TSAKUWAR MARA

Image
DOMIN NARKAR DA TSAKUWAR MARA . GARIN SHAMMAR (cokali 3). HULBA (Cokali 5). GARIN HABBA (cokali 5). BADUNAS (cokali 2 ). Bayan haɗa su guri ɗaya sai a rinƙa ɗiban cokali ɗaya (1) ana dafawa da ruwa kofi ɗaya, bayan ya dahu sai a zuba cokali biyu, a shanye haka za a yi da safe kafin a karya da kuma kafin kwanciya bacci. Allah ya taimaka. Duk mai buƙata muna da shi haɗaɗɗe. Fuad Islamic Herbal Medicine Misau 09031562132 08067676223 No 2. Tamsuguri Turaki Street Misau Bauchi State Nigeria

MAGANIN RIKICEWAR JININ AL'ADA NA MATA

Image
Rikicewar jinin Al'ada ga mata wannan ba baƙuwar matsala bace ko sabuwa ba.  Yawancin mata na fama da irin waɗannan matsalolin, sai dai sukan shiga cikin duhu, su kasa gane dalilan hakan. Matsalar RIKICEWAR jinin Al'ada yana iya faruwa da kowacce mace me aure ce ko marar aure  bazawara ko budurwa duka.  Sai dai kowacce akwai dalilin faruwar nata. Yawanci Matsalar tafi damun Matan aure sakamakon yin allurar ko shan maganin tsarin ƙayyade iyali, saboda Waɗannan magungunan ko allurar ko wannan abin da ake cusa musu a wata jijiya a hannu suna rikita jijiyoyin mahaifa da ma ita mahaifar kanta, ta yadda zata dinga zubar da Jini ba gaira ba dalili, kuma a kasa shawo kan Matsalar. Sai dai wasu kuma matan, matsalar rikicewar jinin Al'adar yana faruwa da su ne sakamakon shigar shaiɗanin aljanin nan me suna jinnul ashiƙ da yake shiga jikinsu don ya hanasu Haihuwa ko kuma aure (Duba rubutuna MATSALOLIN ALJANU DA YADDA ZA A MAGANCE SU za ku samu ƙarin bayani kan wannan Aljanin da dali...

MAGANIN CIWON SUGAR ( *DIABETES*)

Image
MAGANIN CIWON SUGAR ( *DIABETES* ) Daga: Fuad Islamic Medicine Misau 5.0✓✓ Normal 5.5✓✓ Normal 5.8✓✓ Normal Ciwon Sugar (Diabetes) ciwo ne da baya bukatar dogon bayani domin yana cikin manyan cututtukan da suke da matukar Illa ta yanda ya zama tamkar ruwan dare. Wasu ta dalilin wannan ciwo Likitoci sun hanasu cin wasu Abincin domin lafiyarsu. A yau muna tafe da maganin wannan ciwo da yardar Allah ta yanda sugar din jikin mutum zai dai-daita yabkoma Normal Ko da ya kai 11.9 insha Allah zai dawo dai-dai yadda ake bukatarsa. Wasu da yawa Wannan ciwo ya shafi idanunsu basu iya gani sosai koda kuwa kazo kusa da su Wasu hankalinsu ne ma ya taɓa akwai dai manyan illoli da ciwon Sugar ke haifarwa InshavAllah daga wannan hadin matsalan yavzo karshe  zai daidaita yadawo 5.0 ko 5.8 ko 5.5 yakoma normal kenan. Abinda muke Bukata kawai shine * Garin Hulba(Fenugreek powder) 10spoon * Garin Habbatus * Sauda(Blackseed powder)10spoon * Garin Zaitun(Olive powder)10 spoon * Garin Girfat 1...

ZUMA DA TAFARNUWA GA LAIYAR DAN ADAM

Image
Idan ka samu taceccen zuma mai kyau cikin babban cokali daya tare da sala uku na tafarnuwa a yayyan ka shi kanana ko kuma a daka, sai a hada su da zuma. * YADDA ZA A YI AMFANI DA SHI* Asha Clcokali daya da safe kafin a ci abincin safe.  Za a maimaita hakan har tsawon kwana bakwai. * Wannnan hadin zai magance maka:*  1- Matsalan hawan jini. 2- Zai rage yawan kitse a jiki "cholesterols". 3- Zai magance matsakan ciwon gabobi.  4- Zai magance matsalan typhoid.  5- Zai magance dukkan matsalolin zuciya. 6- Zai magance saurin gajiya. 7- Zai magance matsalar haki da yawan nishi.  8- Zai magance matsalar Asma, nymonia da sauran cututtukan da sanyi yake kawowa.  9- Ciwon wuya da dashewar murya.  10- Yana taimako sosai ga masu cutar sugar "Deabetes". 11- Yana kashe duk wasu cututtuka da suke gudana cikin jini. Fuad Islamic Herbal Medicine Misau No 2. Tamsuguri Street Misau Bauchi state Nigeria. +2349031562132 +2348067676223